Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kira Yi Mai Kare Manufofin Kasar Canada

Saboda matsayar da kasar Canada ta dauka na bayyana IRGC a matsayin kungiyar ta’addanci, ma’aikatar harkokin wajen Iran din ta kira yi mai wakiltar manufofin

Saboda matsayar da kasar Canada ta dauka na bayyana IRGC a matsayin kungiyar ta’addanci, ma’aikatar harkokin wajen Iran din ta kira yi mai wakiltar manufofin kasar domin nuna masa rashin amincewa.

Ofishin jakadancin kasar Italiya ne dai yake wakiltar manufofin kasar Canada a Iran, don haka aka kira yi jakadan wannan kasar zuwa ma’aikatar harkokin wajen Iran domin nuna masa kin amincewa da wannan mataki.

Wannan matakin na kasar Canada ya zo ne a lokacin da take daya daga cikin masu kare kungiyar ‘yan ta’adda ta kuma ba su kariya.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai kasar ta Canada ta bayyana Dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda.

Ma’aikatar harkokin wajen ta Iran ta bayyana cewa matakin na kasar Canada yana cin karo da dokokin kasa da kasa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Nasir Kan’ani ya ce, abinda Canada ta yi, yana a karkashin siyasarta ta gaba da kiyayya da jamhuriyar musulunci ta Iran.

Iran din ta kuma gargadi Canada da cewa za ta dauki matakan da su ka dace akan haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments