Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran Ta Kara Haske kan Batun Inganta Sinadarin Uranium Da Zamanta Da Amurka

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta bayyana sabbin ci gaban da aka samu a tattaunawar da aka yi a birnin Roma

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Isma’il Baqa’i ya jaddada cewa: Ana gudanar da zagaye na biyar na tattaunawa ba na kai tsaye ba tsakanin tawagar Amurka da na Iran a cikin yanayi na kwarewa.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran Isma’il Baqa’i ya bayyana a yau Juma’a cewa: Tattaunawar tana gudana cikin kwarewa da kwanciyar hankali, yana mai cewa abin da ake yadawa a kafafen yada labarai hasashe ne da baya da tushe ko inganci kuma baya da bambanci da shaci fadi.

A yau Juma’a da yamma ne aka fara shawarwarin da ba na kai tsaye ba karo na biyar tsakanin Iran da Amurka a hedkwatar wanzar da zaman lafiya ta masarautar Oman da ke birnin Roma fadar mulkin kasar Italiya.

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi da manzon Amurka na musamman Steve Witkoff ne ke jagorantar shawarwarin da masarautar Oman ke shiga tsakani.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments