Hajjatul-Islam Wal Muslimin Muhammad Hassan Abu Turabi da ya jagoranci Sallar juma’a a Tehran a jiya juma’a ya bayyana Imam Khumaini ( r.a) a mastayin daya daga cikin fitattun mutanen da duniyar musulunci ta samu a wannan zamanin.
Hujjatul-Islam Wal Muslimin ya ce, Shakshiyya din Imam Khumaini ta ginu ne akan ilimomi na addini,filiku da falsafa.
Limamin juma’ar na Tehran wanda yake jawabi dangane da zagayowar cikar shekaru 46 daga dawowar Imam Khumaini Iran bayan zaman hijira na shekaru 15 a kasashen waje, ya ce abin alfahari ne yadda wannan rana ta zagayo a daidai wannan lokacin da kungiyoyin gwgagwarmayar musulunci suke kara bunkasa da daukaka a duniyar musulunci.
Hujjatul-Islam Wal Muslimin Abu Turabi ya kuma bayyana cewa abinda yake da muhimmanci a wannan lokacin shi ne ci gaba da aiki akan tafarkin Imam Khumaini cikin tsayuwar daka ba tare da girgiza ba.
Limamin juma’ar na Tehran ya ce kamar yadda abokan gabarmu suke jurewa wajen fuskantarmu, to mu ma ya zama wajibi a gare mu da mu yi tsayin daka wajen fuskantarsu, tare da yin ishara da abinda ya faru a Gaza, da kuma kallafaffen yaki akan Iran yana mai kara da cewa; Ba domin gwagwarmaya ba ta al’ummar Iran da su ka hada da dakarun kare juyin musulunci da sojoji a wancan lokacin, to da abubuwan da suke faruwa na alfahari ga al’ummar Musulmi a wannan lokacin ba su faru ba.