Lebanon: Shahidai Biyu Sanadiyyar Hare-Haren HKI A Lardin Nabatia A Kudancin Kasar

Wani dan kasar Lebanon da matarsa sun yi shahada sanadiyyar hare-haren jiragen yakin HKI a kan motarsu a kauyen Zabdaini na kudancin kasar Lebanon. Tashar

Wani dan kasar Lebanon da matarsa sun yi shahada sanadiyyar hare-haren jiragen yakin HKI a kan motarsu a kauyen Zabdaini na kudancin kasar Lebanon.

Tashar talabijan ta Al-Mayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto dan rahotonta a yankin yana cewa jiragen yakin HKI wadanda ake sarrafasu daga nesa sun kai hari a kan motar dan kasar da matarsa kuma ta kashesu nan take a yayinda wani mutum guda ya ji rauni.

Har’ila yau a lardin Hermel daga gabacin kasar ta Lebanon, dan rahoton Al-Mayadeen ya bayyana cewa jiragen yakin HKI sun aiwatar da hare-hare da dama daga ciki har da kauyen Zagrai.

Tun ranar 27 ga watan Nuwamban shekarar da ta gabata ce HKI take ci gaba da keta yarjeniyar da suka cimma da kungiyar Hizbullah. MDD ta bada sanarwan cewa tun lokacin zuwa yanzu HKI ta kashe mutane 103 a kudancin kasar Lebanon.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments