A safiyar yau lahadi ce mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon suka cilla makamai masu linzami har 50 a kan wasu yankuna a arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran yanakalto tashar talabijin ta Al-Manar ta kungiyar, na fadar haka a safiyar yau Lahadi. Ta kuma kara da cewa makaman sun fada kan Al-Jalil da kuma arewacin tuddan golan na kasar Siriya da aka mamaye.
Banda haka wasu kafafen yada labaran yahudawan sun tabbatar da cewa, wasu makaman sun fada kana garin Beit Hillel da ke arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye.
Labarin ya kara da cewa a halin yanzu HKI tana cikin rudu, saboda tana sauraron yadda raddin JMI da kuma Hizbullah da kuma sauran wadanda suke kawance da su zai kasance, bayan kissan shugaban Hamas da ta yi a Tehran da kuma kissan wani kwamandan sojojin Hizbulla wanda ake kira Sayyid Fu’ad a birnin Beirut a makon da ya gabata da ta yi.