Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon a yau Asabar ta yi ruwan wuta da makaman atilari, Drons makare da makamai da kuma makamai masu linzami.
Tashar talabijin ta Almayadeen ta kasar Lebanon ta nakalto majiyar kungiyar na cewa ta yi amfani da makamai daban daban a hare haren da ta kaiwa wurare daban daban a yankunan Falasdinawa da aka mamaye a shekara 1948 da ke kudancin kasar.
Labarin ya kara da cewa, a Ruwaisat al-Alam a kan tundan Kafarshouba ta cilla makamai masu linzami kan taron sojojin yahudawa wanda ya kai ga asarar rayuka da dukiyoyi tabbasa. Hakama a kusa da sansanin sojoji na Jal al-Alam , ta halaka sojojin yahudawa da dama a wani kauye da ke gaban Alma al-Shaab, da makaman atillari a mnan ma ta kashe sojojin yahudawa da dama.
A shingen Metula kuma sun wargaza wata tankar yaki na sojojin HKI a jiya Jumma’a tare da amfani da da makaman Drone ko jiragen kunan bakin wake makare da abubuwan fashewa. Sannan daga karshe a kusa da barikin sojoji na Zar’it ta yi luguden wuta wanda ya kai ga halakar sojojin yahudawa.
Kungiyar ta bayyana cewa hare haren na maida martani ne da kuma tallafawa mutanen Gaza wadanda HKI takewa kissan kiyashi.