Lebanon: An Samu Karin Fashewar Wasu Na’urorin Sadarwa Wanda Ya Yi Ajalin Mutane 9

Na’urorin da aka fi sani da Walkie-talkies, sun fashe ba zato ba tsammani a wannan  Laraba a yankuna da dama a Lebanon, a wani harin

Na’urorin da aka fi sani da Walkie-talkies, sun fashe ba zato ba tsammani a wannan  Laraba a yankuna da dama a Lebanon, a wani harin da Isra’ila ta sake kaiwa.

Na’urorin ICOM V82s, sun fashe ne ba da dadewa ba, kuma saboda na’urorin da ke dauke da batir lithium masu iya konewa ne, sun ta fashewa inda lamarin ya yi muni matuka.

Fashe-fashen sun haifar da gagarumar gobara a cikin motoci, babura, gidaje, da kantuna a duk fadin kasar Lebanon. Har yanzu ba a tantance iyakar raunukan ba.

Wata na’ura ta  fashewa ne a yayin da ake gudanar da jana’izar wani mutum da ya yi shahada a wani mummunan hari makamancin wannan da Isra’ila ta kai a wannan  Talata, inda jama’a da dama suna a kusa da wanda yake dauke da na’urar, wanda hakan ya yi sanadin jikkatar mutane da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments