Sakataren Majalisar Koli ta tsaron kasar Iran Dr. Ali Larijani ya bayyana haka ne a wani sako da ya walalfa a shafinsa na sadarwa dangane da sako fursunonin Falasdinawa da aka yi.
Haka nan kuma ya ce: ‘Yan Sahayoniya sun ga hotunan gagarumar tarbar da aka yi wa Fursunonin Falasdinawan da hakan yake sake tabbatar musu da cewa; Kungiyar Hamas da gwagwarmaya suna da karbuwa da farin jini a tsakanin Falasdinawa bayan gushewar shekaru biyu na kazamin yaki.
A jiya da safe ne dai al’ummar Falasdinu su ka tarbi Falasdinawan da HKI ta sako daga gidajen kurkukunta a karkashin yarjejeniyar kawo karshen yaki da ta kunshi musayar fursunoni.