Search
Close this search box.

Landan: Jaridar Guardian Ta ce Yake-Yaken Makamashi Zasu Bullu A Kasashen Turai Nan Gaba

Jaridar Guardian ta kasar Burtania ta bayyana cewa mai yuwa a fara yake yaken masu nasaba da makamashi a kasashen Turai nan gaba sabosa tsadar

Jaridar Guardian ta kasar Burtania ta bayyana cewa mai yuwa a fara yake yaken masu nasaba da makamashi a kasashen Turai nan gaba sabosa tsadar farashin makamashi da kuma rikicin da kasashen nahiyar suke yi da kasar Rasha a Ukraine.

Labarin ya kara da cewa, Andrey Kobolev shugaban kamfanin man fetur da iskar gas na kasar Ukraine, ya bayyanawa jaridar Guardian kan cewa a halin yanzu gwamnatin kasar Rasha tana son samar da yakin ‘makamashi’ tsakanin kasashen turai, sannan nasarar kasar Rasha kan Ukraine a yakin da suke fafatawa zai hadda rikita kasuwar makamashi a kasashen Turai.

Ya kamala da cewa, idan an ci gaba da lalata cibiyoyin man fetur da da gasa na kasar Ukraine a yakin da take fafatawa da Rasha to kuwa bayan yakin za’a gamu da matsalolin makamashi a kasashen na Turai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments