Laifukan da ake gudanarwa a gabar tekun Siriya: Cin zarafin ya kai ga laifukan yaki!
Rahotonni sun bayyana cewa; Kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan kasar Siriya ya fitar ya ce: Rikicin kabilanci da ya faru a gabar tekun Siriya ya kunshi cin zarafi da ya kai ga laifukan yaki.
Rahoton ya kara da cewa; Rikicin addini ya shafi mabiya darikar Alawiyya ne, inda aka kashe fiye da mutane 1,400 Alawiyyawa a rikicin addini da suka hada da daukacin iyalai da mata da yara da kuma tsofaffi a gabar tekun Siriya. Bugu da kari, an samu rahotannin kone-kone, sace-sace da kuma wulakanta gawarwakin da wasu ‘yan bindiga suka aikata.
Rahoton ya bukaci gwamnatin rikon kwarya ta Siriya da ta fadada kokarin da ake yi na Sanya ido kan masu aikata laifukan cin zarafin al’umma da sunan addini.