Kwamitin Sulhu Ya Nuna Takaici Kan Harin Da Aka Kai Kan Dakarunsa A Lebanon

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da hare-haren baya-bayan nan kan tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Lebanon a daidai lokacin

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah-wadai da hare-haren baya-bayan nan kan tawagar wanzar da zaman lafiya a kasar Lebanon a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hari kan sansanonin ta da gangan.

A cikin wata sanarwa da ya fitar, kwamitin mai mambobi 15 ya “yi Allah wadai da al’amura da dama da suka shafi dakarun na (UNIFIL) da kuma jikkata wasu a makonnin da suka gabata.”

Har ila yau, ya bukaci bangarorin da ke rikici da juna a kasar Lebanon da su dauki dukkan matakan kare ma’aikatan UNIFIL da wurarensu.

Isra’ila dai na ci gaba da kai hare hare a fadin kasar Lebanon bayan da gwamnatin kasar ta kaddamar da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza.

Akalla mutane 3,287 ne suka mutu yayin da wasu 14,222 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Lebanon tun farkon watan Oktoban 2023, a cewar ma’aikatar lafiya ta kasar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments