Kwamandan sojoji masu kare iyakokin Iran ya Kanar Ali Akbar Jawidan ya bayyana cewa; a cikin makwanni kadan da su ka gabata ‘an kama makamai na yaki da aka yi kokarin fasakwaurinsu zuwa cikin Iran da yawansu ya kai 165.
Kanar Jawidan ya bayyana hakan ne a yau Asabar a yayin da ya kai ziyarar aiki a barikokin sojoji da suke akan iyakokin Iran na yamma, yana kuma mai yin tsokaci akan nasarorin da jami’an dake tsaron kan iyakokin suke samu na dakile ayyukan fasakwaurin makamai.
Haka nan kuma ya bayyana cewa; A halin da ake ciki da akwai cikakken tsaro akan iyakokin Iran,domin jami’an tsaro suna cikin Shirin ko-ta-kwana domin kare iyakoki.
Jami’in sojan ya kuma ce; Jami’an tsaron kan iyaka suna cikin shiri fuskantar kowace irin barazana, ba kuma za su bar kowane mahaluki ya cutar da kasa ba.