Ya zuwa yanzu da aka cika kwanaki 60 da HKI ta shelanta yaki gadan-gadan akan kasar Lebanon, ta kai hare-hare masu tsanani akan garuruwan kudancin Kasar da kuma Unguwar Dhahiya dake birnin Beirut.
A jiya Laraba ma’aikatar kiwon lafiya ta kasar Lebanon ta sanar da cewa adadin wadanda su ka yi shahada sanadiyyar hare-haren HKI sun kai 3000, yayinda wadanda su ka jikkata sun kai 13.000.
A yau Alhamis ma dai jiragen yakin HKI sun kai hare-hare a lokuta mabanbanta akan yankin “Harat-Harik” dake unguwar Dhahiya da nan ne babban zangon kungiyar Hizbullah a cikin birnin Beirut.
A can kan iyaka kuwa, mutane 3 ne su ka yi shahada yayin da wasu 5 su ka jikkata a yau Alhamis a garin “Sha’itiyyah” a gundumar Sur.
Wasu yankunan da jiragen yakin HKI su ka kai wa hare-hare a yau Alhamis sun hada “Burjul-Shimal” da kuma garin “Arnu”.
A garuruwan Ansariyah da Adlun an sami shahidi daya, haka nan kuma ‘yan mamaya sun kai wasu hare-haren da manyan bindigogi akan garin Shabil da Qatrani a yankin Jazzin.
A garin Sur mutane 13 ne su ka yi shahada a harin da ‘yan sahayoniya su ka kai a jiya Laraban,wasu 44 kuma su ka jikkata.