Kutun Kasa Da Kasa Ta ICC Ta Ce Zata Ci Gaba Da Ayyukan Ta A Duniya Duk Tare Da Takunkuman Amurka

Kotun hukunta manya-manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta yi allawadai da takunkuman da gwamnatin Amurka ta dorawa kotun, ta kuma kara da cewa

Kotun hukunta manya-manyan laifuka ta kasa da kasa ICC ta yi allawadai da takunkuman da gwamnatin Amurka ta dorawa kotun, ta kuma kara da cewa zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya kamar yadda ta saba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa kotun ICC kotu ce wacce take karban koke-koke na mutane da kasashe a duk fadin duniya, amma wacce gwamnatin Amurka ta ke son takaita ikonta don tallafawa HKI a yakin da take fafatawa da Falasdinawa wadanda ta mamaye kasarsu fiye da shekaru 76 da suka gabata.

A ranar Alhamis da ta gabata ce shugaban kasar Amurka Donal Trump ya sanya hannu a kan wata doka wacce ta dorawa kotun ta ICC takunkuman tattalin arziki masu tsanani da kuma hana jami’anta tafiye-tafiye zuwa Amurka. Shugaban ya ambaci sammacin da kotun ta fitar na kama firai ministan HKI Benyamin Natanyahu wanda ya aikata laifukan yaki a gaza, a matsayin hujjarsa ta dorawa kotun wadannan takunkuman.

Kasashe kimani 79 daga ciki har da Canada, Mexico da Najeriya sun ja hankalin kasashen duniya kan cewa wadannan takunkuman kan ICC zai sa a kara aikata laifuffukan yaki a duniya. Sanna sai wargaza dokokin kasa da kasa da dama.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments