Yayin da gwamnatin yahudawan sahyoniya ke ci gaba da kaddamar da farmaki na soji a kan fararen hula a yankin Rafah da ke kudancin zirin Gaza, kungiyoyin kare hakkin bil adama na kasa da kasa guda 20 sun yi tir da laifukan gwamnatin yahudawan Isra’ila.
A rahoton da tashar Al Jazeera ta bayar, manyan kungiyoyin kare hakkin bil’adama 20 daga sassan duniya sun sake neman kasashe da su dakatar da harin kisan kare dangi na Isra’ila a Rafah.
Amnesty International, Oxfam, ActionAid da sauran kungiyoyin kare hakkin bil’adama na duniya, sun yi Allah wadai da gazawar kasashen duniya wajen kasa dakatar da ayyukan yaki na Isra’ila Rafah.
Wadannan kungiyoyi sun jaddada a cikin sanarwar tasu cewa, harin da Isra’ila ta kai a Rafah ya kara tsananta muwuyacin halin da al’ummar Gaza suke ciki, da kuam kawo tarnaki ga ayyukan jin kai a yankin.
Sanarwar ta ce: Kasashen duniya na da alhakin daukar mataki cikin gaggawa domin kawo karshen keta dokokin kasa da kasa da Isra’ila take yi a Gaza.
A gefe guda kuma, majiyoyin labarai sun bayar da rahoton a safiyar yau Alhamis game da harin da sojojin yahudawan sahyoniya suka kai a yankuna daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan da kuma rikicin da ya barke tsakaninsu da Palasdinawa.
Majiyoyin cikin gida sun sanar da cewa dakarun yahudawan sahyuniya sun kai hari a yankuna daban-daban na yammacin gabar kogin Jordan.
Shafin yada labarai na Aljazeera ya bayar da rahoton cewa, dakarun gwagwarmayar Palastinawa sun yi arangama da dakarun gwamnatin mamaya a garuruwan Tubas, Qalqilyeh, Tulkarm da kuma Baitalami.
Rahotanni sun nunar da cewa sojojin gwamnatin mamaya sun kashe wasu Falasdinawa uku a garin Tulkarem, yayin da wasu Falasdinawa biyu suka jikkata a Qalqilya.