Kungiyar yan ta’adda ta Daesh ko ISIS wacce take kafirta musulmi ta dauki alhakin kashe musulmi shia wadanda suke makokin shahadar Imam Hussain (a) jikan manzon All..(s) kuma limami na 3 daga cikin limamai daga iyalan gidan manzon All..(s) a wani masallaci a birnin Muscat na kasar Omman.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto wani bayani wanda kungiyar yan ta’addan ta buga a shafinta na Telegram a jiya Talata, har ma ta sanya wani hoton bidiyo wanda yake nuna lokacinda suka kai hare hare kan musulmi shia masu makokin ashoora.
Kungiyar ta kara da cewa mutane uku daga cikin mabiyansu ne suka budewa masu makokin Imam Hussain (a) a Muscat wuta inda suka kashe wasu daga cikinsu.
Labarin ya kara da cewa yan ta’addan sun kai harin ne a unguwar wadi-Kabir na birnin Muscat inda suka yi harbi da bindiga suka kashe mutane akalla 9, daga cikinsu akwai yan kasar Pakistan da dan kasar Indiya guda, da kuma dansandan kasar omman guda daya.
Har’ila yau sun yi musayar wuta da jami’an tsaron kasar. Sai dai babu labarin ko an kashesu ko an kama su.