Kungiyar OIC: Kisan Haniyya a cikin Iran keta hurumin kasar ne

Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Nashrah ya bayar da rahoton  cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da sanarwa ta karshe bayan taronta

Shafin sadarwa na yanar gizo na Al-Nashrah ya bayar da rahoton  cewa, kungiyar hadin kan kasashen musulmi ta fitar da sanarwa ta karshe bayan taronta a birnin Jeddah, inda ta yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi wa shahid Ismail Haniyya , tsohon shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas a birnin Tehran, tare da bayyana cewa: muna sane da cewa Isra’ila ce ke da alhakin aikata wannan zalunci.

Kungiyar ta yi ishara da cewa kisan gillar da aka yi wa Haniyya laifi ne na wuce gona da iri da kuma keta dokokin kasa da kasa karara, wannan kungiya ta kara da cewa: Kisan Haniyyah wani hari ne a cikin hurumin kasar Iran, wanda ya sabawa dukkanin dokoki na kasa da kasa.

Mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bagheri Keni ya bayyana a yayin halartar taron kungiyar hadin kan kasashen musulmi da aka yi a birnin Jeddah cewa, kisan gillar da aka yi wa Ismail Haniyeh a birnin Tehran ba zai taba yiwuwa ba tare da goyon bayan Amurka ba.

Ya kara da cewa: Tehran za ta yi amfani da hakkinta wajen kare kanta daga zaluncin Isra’ila kuma ba ta da wani zabi da ya wuce mayar da martanin da ya dace kan hakan.

Bagheri ya yi nuni da cewa, Iran ba ta fatan ganin rikici ya bazu a sauran yankuna na gabas ta tsakiya, amma kuma babu abin da ya rage a gare ta illa mayar da mummunan martani a lokacin da kuma wurin da ta ga ya dace.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments