Kungiyar MSF Ta Gargadi HKI Kan Jefa Gaza Cikin Hatsarin Mutuwa Tare Da Haramtata A Yankin

Kungiyar ‘Doctors Without Borders (MSF) ta gargadi HKI kan cewa idan ta ci gaba da hana kungiyoyin bada agaji a gaza, to dai dai ne

Kungiyar ‘Doctors Without Borders (MSF) ta gargadi HKI kan cewa idan ta ci gaba da hana kungiyoyin bada agaji a gaza, to dai dai ne da tana son ganin mutuwar falasdinawa a dubbansu a gaza.

Tashar talabijan ta Aljazeera ta kasar Qatar ta nakalto wani Jami’in kungiyar Craig Kenzie

 Yana fadar haka a yau Lahadi ya kuma kara da cewa HKI ta haramta kungiyoyin bada agaji da dama a gaza daga ciki har da MSF saboda mun ki bayyana sunayen ma’aikatammu a cikin falasdinawa. Kungiyar ta ki yin haka ne don HKI zata kashesu. Ko ta cutar da su.

Craig Kenzie  ya bayyana cewa kungiyar tana ayyuka masu yawa a gaza wanda ya hada da ruwa sha mai tsabta lita miliyton 4.5 kashi 20% kadajen asbiti, kula da 1/3 na haihuwa sannan da kula da marasa lafiya 800,000 a ko wace shekara.

Ya ce idan wannan ya yanke yana nufin karin musiba a Gaza, don cututtuka zasu Kiara yaduwa haka ma yawan mutuwa.

Labarin ya kara da cewa, HKI tana neman duk wata hanya ta kashe falasdinawa a Gaza don kwace yankin daga hannunsu da gaggawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted