Search
Close this search box.

Island Na Dab Da Amincewa Da Falasdinu A Matsayin Kasa Mai Cikakken Yenci

Gwamnatin kasar Island tana daba da amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta da kuma ciekken yanzin. Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya

Gwamnatin kasar Island tana daba da amincewa da kasar Falasdinu mai zaman kanta da kuma ciekken yanzin.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ministan harkokin wajen kasar Island Micheál Martin yana fadar haka, ya kuma kara da cewa kafin karshen watan mayun da muke ciki gwamnatin kasar Island zata amince da kasar Falasdinu a matsayin yentacciyar kasa mai zaman kanta

Kafin haka dai a ranar 10 ga watan mayun da muke ciki, ministan ya bayyana a taron babban zauren MDD dangane da samar da kuduri mai tabbatar da kasar Falasdinu a matsayin cikekken manba a majalis kan cewa lokaci yayi da za’a bawa mutanen Falasdinu damar fayyace makomar kasarsu.

Ya kara da cewa muna son MDD ta amince da kasar Falasdinu a matsayin kasa ta 194 a majalisar. Duk da cewa kasar Island ta amince da samuwar HKI amma kuma bai hanata ta bukaci a kafa kasar Falasdinu a kan iyakokin shekara 1967 ba. A halin yanzu dai kasar falasdinu mamba ce mai sanya ido a babban zauren majalisar, inda bata da hakkin kada kuri’a ko rike wani matsayi a majalisar.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments