Shugaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran Muhammad Eslami ya bayyana cewa a taron kasa da kasa wanda Iran ta shirya dangane da fasahar nukliya a birnin Esfahan na tsakiyar kasar, an warware dukkan matsalolin da ke tsakanin ta da hukumar IAEA sai guda biyu kacal.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Islami yana cewa a taron kasa da kasa kan makamashin nukliya da aka gudanar a birnin Esfahan a karon farko JMI ta bayyanawa duniya kan cewa a shirye take ta yi musayar fasahar Nukliya da take da shi da sauran kasashen duniya. Kuma an sami takardu dangane da fasahar nukliya har kimani 600 a taron. Kuma an amince da kimani 400 daga cikinsu.
Shuagaban hukumar makamashin nukliya na kasar Iran ya kammala da cewa a taron na Esfahan ne hukumarsa ta tattauna da jami’an hukumar IAEA mai kula da al-amuran nukliya a duniya, inda suka sami nasarar warware mafi yawan matsalolin da tsakanin bangarorin biyu in banda guda biyu.