Kungiyar hadakar kasashen nan uku na Sahel da ake kira (AES), a takaice, za ta gudanar da taron shugabannin kasashen irinsa na farko a birnin Yamai na Jamhuriyar Nijar ranar Asabar.
Taron zai hada da shugabannin kungiyar kasashen da suka hada da Kanal Asimi Goita na Mali, da Kyatin Ibrahim Traore na Burkina faso da kuma Abdurahmane Tinai na Nijar.
Wata sanarwa da hukumomin mulkin sojin Nijar suka wallafa a shafukan sada zumunta ta bukata al’ummar birnin Yamai dasu fito dafifi yau bayan sallar Juma’a domin yi wa jagororon dake fafatukar samar da ci gaba da tsaro a yankin kyakyawan tarbe.
Taron na kasashen uku na yankin da suka balle daga kungiyar Ecowas a farkon shekarar nan, na zuwa ne ganabin wani taron kungioyar ta Ecowas a ranar Lahadi mai zuwa.
A ranar 28 ga watan Janairun 2024, ne kasashen Burkina faso, Mali da kuma Nijar, suka fitar da sanarwa bi da bi domin bayyana matakin raba gari da kungiyar ci gaban tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ta ECOWAS ko CEDEAO.
Kasashen na masu zargin kungiyar ta ECOWAS, da rashin adalci, da kaucewa muhimman maradun kafa ta, hasali ma da zama ‘yar amshin shatan shatan kasashen yammacin duniya domin cin amanar kasashe mambobinta da kuma kasawa wajen dafawa yakar ayyukan ta’addanci da ya addabi yankin.