Amnesty Ta Zargi Gwamnatin Tanzaniya Da Musgunawa ‘Yan Adawa

Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar Kungiyar

Kungiyar kare hakkin dan Adama ta Amnesty International ta ce: Gwamnatin Tanzaniya ta wurga yanayin tsoro tare da tsananta danniya gabanin babban zaben kasar

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi mahukuntan Tanzaniya da haifar da yanayin tsoro da kuma tsananta danniya gabanin babban zaben da aka shirya yi a ranar 29 ga watan Oktoba, tare da yin amfani da dabarun yaki da ‘yan adawa, ‘yan jarida, kungiyoyin farar hula, da masu kare hakkin bil’adama.

Amnesty International ta bayyana cewa: Gwamnatin shugaba Samia Hassan na ci gaba da ayyukanta na danniya da suka hada da kama mutane ba bisa ka’ida ba, tilasta bacewar mutane, da kuma kashe-kashen ba bisa ka’ida ba, ba tare da hukunta wadanda suka aikata laifuka ba.

Kungiyar ta yi nuni da yadda ake ci gaba da kai hare-hare kan shugabannin ‘yan adawa, inda aka haramtawa fitattun ‘yan takarar shugaban kasa tsayawa takara, yayin da wasu kamar Tundu Lissu ke fuskantar shari’a kan tuhume-tuhumen siyasa da suka hada da hada baki da furta kalaman karya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted