Kungiyar Jihadul-Islami Ta Falasdinu Ta Sanar Da Shahadar  Abu Hamza Kakakin Dakarunta Na Sarayal-Kudus”

A jiya Talata ne dai kungiyar ta Jihadul-Islami ta kaddamarwa da al’ummar Musulmi  shahadar Naji Abu Saif, wanda ake yi wa lakbi da Abu Hamza,

A jiya Talata ne dai kungiyar ta Jihadul-Islami ta kaddamarwa da al’ummar Musulmi  shahadar Naji Abu Saif, wanda ake yi wa lakbi da Abu Hamza, da ya kasance kakakin dakarun “Sarayal-Kudus” bayan da ‘yan sahayoniya su ka yi masa kisan gilla tare da iyalansa da iyalan dan’uwansa.

 A bayanin da ta fitar, kungiyar ta Jihadul-Islami ta ce; Duniya ta yi sanayya da sautin shahidin wanda ya kasance sauti ne na gwagwarmaya da ba ya tsoron wani zargi akan tafarkin Allah, wanda kuma Allah ya yi wa baiwar fasahar zance da kuma jarunta da kare hakkokin al’ummarmu ta Falasdinu.

Kungiyar ta kuma ci gaba da cewa,kisan gillar da ‘yan sahayoniyar su ka yi wa Abu Hamza wani sashe ne na jerin kisan kiyashin da suke yi wa al’ummar Falasdinu wanda ya yi sanadiyyar shahadar Falasdinawa da dama, kananan yara maza da mata.

Kungiyar ta Jiahdul-Islami ta kuma ce;Amurka ce take karfafawa ‘yan sahayoniya gwiwa da kuma taimaka musu akan laifukan da suke yi, tare da bayyana mamaki akan yadda duniya ta sanya idanu tana kallo.

Sai dai kungiyar ta ce; Abinda yake faruwa babu abinda zai karawa Falasdinawa sai tsayin daka da jajurcewa wajen kare hakkokinsu da dakile manufofin abokan gaba baki daya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments