Kungiyar Hizbullahi Ta Tarwatsa Hedikwatar Hukumar Leken Asirin Yahudawan Sahayoniyya

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba makami mai linzami kirar Qadir 1 kan hedikwatar hukumar leken asiri ta Mossad a haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar

Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta harba makami mai linzami kirar Qadir 1 kan hedikwatar hukumar leken asiri ta Mossad a haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da kai hari kan hedikwatar hukumar leken asirin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta Mossad da ke wajen birnin Tel Aviv, hedkwatar ce da ke da alhakin kashe-kashen gillar shugabannin kungiyar ta Hizbullah da kuma tayar bama-bamai na Beijer da hanyar sadarwar Lebanon ta hanyar makami mai linzami na Qadir 1, wanda hakan ya shiga mataki karon farko tun daga farkon ayyukan tallafawa al’ummar                   Falasdinu.

A matanin da sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta fitar ta bayyana cewa: Domin jaddada goyon baya ga al’ummar Falastinu masu tsayin daka a Zirin Gaza da kuma goyon bayan gwagwarmayarsu mai martaba gami da kare kasar Lebanon da al’ummarta, ‘yan gwagwarmayar Hizbullahi sun kaddamar da farmaki a safiyar yau Laraba 25 ga watan Satumban shekara ta 2024 da karfe 6:30 na safe, harin makami mai linzami na “Qadir 1” kan hedkwatar rundunar hukumar leken asirin gwamnatin ‘yan sahayoniyya ta Mossad da ke wajen birnin Tel Aviv, hedkwatar da ke da alhakin kashe-kashen gillar shugabanni da kuma kai hare-haren bam kan wurare masu muhimmanci na kungiyar ta Hizbullah.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments