Kungiyar Hizbullahi Ta Ce Mayar Da Martaninta Kan Yahudawan Sahayoniyya Zai Fi Zafi

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta lashi takwabin ruguza haramtacciyar kasar Isra’ila a kan kawunan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya Mamba a majalisar tsakiya ta kungiyar

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta lashi takwabin ruguza haramtacciyar kasar Isra’ila a kan kawunan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya

Mamba a majalisar tsakiya ta kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta kasar Lebanon Sheikh Hassan al-Baghdadi ya bayyana a jiya Lahadi cewa: Idan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya na son rusa kasar Labanon daga nesa, to kungiyar Hizbullahi zata ruguza haramtacciyar kasar Isra’ila ce a kan kawunan yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya.

A hirar da ya yi da kafar yada labarai ta Mehr ta kasar Iran, Sheik Al-Baghdadi ya ce: Kungiyar Hizbullah tana da martani mai muni kan haramtacciyar kasar Isra’ila da kuma sojojin sa-kai da za su iya shiga kasar Falasdinu da aka mamaye, yayin da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya ba su da sojojin da suke da karfin shiga cikin kasar Lebanon.

Hassan Al-Baghdadi ya ci gaba da cewa: A kodayaushe suna tsammanin cewa wannan gwamnatin mamaya ba zata dade ba, kuma wannan hasashe yana da dalilai nasa, wanda mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne wautar shuwagabannin yahudawan sahayoniyya, kuma rayuwar gwamnatin ‘yan mamaya ta fara kirgawa zuwa karshenta, don haka wannan gwamnatin ‘yan mamaya ta wucin gadi ce da zata zo karshe nan ba da jimawa ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments