Rahotanni daga Lebanon na cewa, kungiyar Hezbollah, na ci gaba da kara fadada ayyukanta na soji a kan yankunan arewacin Falastinu da Isra’ila ta mamaye, da kuma fuskantar yunkurin Isra’ila na kutsawa kudancin kasar Lebanon.
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon – Hizbullah tana ci gaba da gudanar da ayyukanta na yakar haramtacciyar kasar Isra’ila, tare da fadada da’irar wutar da take antawayawa a kan dandanzon sojojin yahudawa a arewacin Palastinu da ta mamaye, da kuma fuskantar yunkurin kutsawa da Isra’ila ke yi a kudancin kasar.
A cikin wannan yanayi ne, da misalin karfe 07:00 na safiyar yau Juma’a, Mayakan Hizbullah suka kai hari da makami mai linzami a yankin “Krayut” dake arewacin Haifa.
Sai kuma da karfe 08:20 na safe (lokacin gida), mayakan na Hizbullah sun yi ruwan bama-bamai a birnin Sabad da makamai amsu linzami.
Da misalin karfe 9:15 na safe, mayakan Hizbullah sun kai hari a sansanin sojojin yahudawan haramtacciyar Kasar Isra’ila a kudancin Kiryat Shmona da makami mai linzami.
Bayan haka, Hizbullah ta nufi sansanin “Ilania” tare da harba makami mai linzami da karfe 10:20 na safe.
Da misalin karfe 11:24 ne mayakan Hizbullah suka kai hari a yankin Ruwaisat al-Alam da ke cikin tsaunukan Kafr Shuba da manyan makamai na atilare a akan sojojin yahudawan Isra’ila.