Kungiyar Hizbullah Ta Cilla Makamai Masu Linzami Kan Garin Tzuriel Moshab Na Yahudawan Sahyoniyya

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun yi ruwan makamai masu linzami a kan garin Tzuriel-Moshav da ke arewacin yankin shekara ta 1948 na kasar

Mayakan kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon sun yi ruwan makamai masu linzami a kan garin Tzuriel-Moshav da ke arewacin yankin shekara ta 1948 na kasar Falasdinu da aka mamaye.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tashar talabijin ta 14 ta HKI na bada labarin ruwa makamai masu linzamin da suka fada kan garon Moshav na yankin Galilee wanda kuma yayi barna masu yawa.

Hukumar bada agajin gaggawa ta HKI  ‘Magen David Adom (MDA)’  ya bada labarin cewa mutane biyu sun ji rauni kuma an kai su da gaggawa zuwa Asbitin galilee da ke yankin.

Labarin ya kara da cewa wannan shi ne karon farko wanda kungiyar ta yi ruwan makamai masu linzami a kan garin mai mutane kimani 400.

Labarin ya kara da cewa kungiyar ta kai wadan nan hare haren ne a matsayin maida martini ga hare haren da sojojin  HKI suka kai a kudancin kasar Lebanon.

Banda haka dakarun na Hizbullah sun lalata na’urorin liken asiri na ‘Rada’ da suke yankin Al-Raheb, inda suka lalata na’urorin liken asirin da HKI take da su a gonakin Shebaa na yakin.

Kafin haka dai mayaklan kungiyar sun lalata na’urorin liken asirin yahudawan da da ke Al-rabeh amma yahudawan suka girka wasu sabbi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments