Kungiyar gwagwarmayar musulunci ta Lebanon tana cigaba da kai wa sansanonin sojan HKI hare-hare da makamai mabanbanta.
Tashar talabijin din \almayadin’ mai watsa shirye-shieyenta daga kasar Lebanon ta bayar da labarin cewa;kungiyar ta Hibzullah ta kai wasu hare-hare a jiya Alhamis akan sansanin “Rustayil-Alam’wanda yake matsugunin ‘yan share wuri zauna dake ‘al-mutlahha’.
Hare-haren na kungiyar ta Hizbullah dai suna zuwa ne a matsayin mayar da martani ga wuce gona da irin ‘yan sahayoniya akan Lebanon da kuma taya Falasdinawa yaki.