Kungiyar Hamas ta yaba da rawar da Iran ke takawa wajen tallafawa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yanci kai
Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araqchi ya gana da wata tawaga daga jagororin kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas, karkashin jagorancin shugaban majalisar gudanarwa (wanda aka kafa bayan kisan jagoran kungiyar Yahya Sinwar) Mohammed Darwish, a babban birnin Qatar, Doha a jiya Alhamis.
Sanarwar da kungiyar Hamas ta fitar ta bayyana cewa, tawagar kungiyar ta hada da shugabannin Khalil Al-Hayya, Hussam Badran, Izzat Al-Rishq da Basem Na’im.
Darwish ya yaba da rawar da Iran ta taka wajen tallafa wa al’ummar Falasdinu masu neman ‘yancin kai, yana mai jaddada cewa: “Harin Daukan Fansa naAmbaliysar Al-Aqsa Mai Albarka” wani ci gaba ne a yunkurin al’ummar Falasdinu na fatattakar ‘yantar da kai daga ‘yan mamayar Isra’ila.”
Ya kuma jaddada cewa: “Shirye-shiryen da mafarkin da gwamnatin mamayar Isra’ila suke yi na kawar da al’ummar Falasdinu daga kasarsu ta gado ta hanyar kaddamar da yaki da kashe-kashe ta kowane irin nau’in ta’addanci, ba zasu taba amfani ba, kuma al’ummar Falasdinu sun kafu ne a cikin kasarsu, suna sadaukar da kai ne domin hakkinsu da Qudus da kuma Masallacin Al-Aqsa”.