Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta shirya wata zanga-zanga da Falasdinawa ke jaddada cewa: babu halacci ga ‘yan mamaya kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da gwagwarmaya
Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta jaddada cewa: Haramtacciyar kasar Isra’ila ba ta da halacci ko kuma wani ikon mallakar wani yanki na Falasdinu da ta mamaye, kuma al’ummar Falastinu za su ci gaba da kare kansu ta hanyar gudanar da gwagwarmaya har sai sun kwato dukkanin Falastinu tare da kafa kasar Falasdinu mai cikakken ‘yanci kai wacce Qudus zata kasance a matsayin babban birninta.
A yayin bikin cika shekaru 77 da kafuwar Nakba, -boren Falasdinawa na farko- kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta bayyana cewa: “Ba za a yi wani sabon Nakba ko sake tilastawa Falasdinawa gudun hijira ba, hadin kan al’umma da gwagwarmaya zasu dakile duk wani makircin makiya, kuma zasu ci gaba da kalubalantar duk wani makirci, domin hakan ne zai karya lagon ‘yan mamaya da tabbatar da samun ‘yanci da komowar ‘yan gudun hijira kasarsu ta gado.