Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ta sanar da sharudan sakin dukkan fursunonin Isra’ila da take tsare da su
Wani jami’in Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas ya ce: Kungiyar a shirye take ta sako daukacin fursunonin Isra’ila domin tsagaita bude wuta da ficewa daga Gaza, kamar yadda wani rahoto da tashar talabijin ta Alkahira ta fitar.
Jami’in na kungiyar Hamas ya kara da cewa: A ranar litinin din nan ne haramtacciyar kasar Isra’ila ta ci gaba da kawo cikas ga yarjejeniyar tsagaita bude wuta da kuma yin watsi da alkawurran da ta dauka, yana mai cewa kungiyar Hamas ta tabbatar wa masu shiga tsakani da “bukatar bayar da lamuni don tilastawa gwamnatin mamayar Isra’ila aiwatar da yarjejeniyar.”
Yana mai bayyana cewa, “Hamas ta yi aiki mai kyau kuma tare da babban sassauci gami da aiki da ra’ayoyin da aka gabatar mata a cikin shawarwarin tsagaita wuta da musayar fursunonin Isra’ila.”