Kungiyar gwagwaramaya ta Hamas a zirin Gaza ta bada sanarwan cewa kissan kiyashin da sojojin HKI suka aikata a asbitin Kamal Adwan a arewacin Gaza abin yin allawadai ne, kuma laifin yaki ne.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta kara da cewa, a daren jumma’a ne sojojin yahudawan suka farwa asbitin Kamal Adwan, asbiti tilo da ya rage a yankin arewcin gaza, inda suka kashe mutane 53 a cikin asbitin, wadanda suka hada da marasa lafiya likitoci da kuma wadanda suke samun mafaka a cikin asbitin.
Banda haka sojojin yahudawan sun tilastwa kowa barin asbitin daga cikin har da jami’an kiwon lafiya.
A wani labarin da asbitin ya watsa a shafinsa na Telegran ya kara da cewa sojojin yahudawan sun konan dukkan gineginen asbitin ta yadda a halin yanzu babu abinda ya rage mai amfani a cikinsa.
Daga karshe kungiyar ta kammala da cewa gwamnatin HKI da kuma Amurka wacce take tare da ita ne suka da alhakin duk abinda ya faru.