Kungiyar Hamas wacce take iko da zirin gaza ta bukaci masu shiga tsakanin Amurkawa su ngamtar da ita kan cewa HKI zata dakatar da yaki ta kuma fice daga zirin gaza. Amma shawarar da Steve Witkoff ya gabatar bata kunshi wani abu wanda zaia gamsar da kungiyar ta amince da wani sulhu ba.
Jihad Taha kakakin kungiyar ya bayyana cewa Hamas tana nazarin shawarar da Witskoff ya gabatar da tsagaita wuta a gaza wanda ya amince da dakatar da wuta na wucin gadi sannan a sake komawa yaki da kuma shigo a kayakin agaji. Y ace shawarar bata ambaci ficewar sojojin HKI daga yankin ba.
Taha ya bayyana cewa shawarar bata da wani abin dogaro wanda Hamas da kungiyoyin masu gwagwarmaya zasu riki na tsagaita wuta a gaza. Amma dukm da haka suna nazarinsa kuma zasu bayyana ra’yinsu nan gaba.
Ya Zuwa yanzu dai sojojin yahudawan sun kashe Falasdinawa fiye da 54000 a cikin shekara da rabi da suke fafatawa.