Kungiyar Hamas Ta Bude Ofishinta Na Farko A Kasar Iraki

Bude wannan ofishin na Hamas a Iraki ya zo ne a daidai lokacin da bangarenta ta soja, “Kassam” yake cigaba da yaki da sojojin mamayar

Bude wannan ofishin na Hamas a Iraki ya zo ne a daidai lokacin da bangarenta ta soja, “Kassam” yake cigaba da yaki da sojojin mamayar HKI na tsawon watanni 8 a jere.

Ana sa ran cewa a kwanaki kadan masu zuwa ne za a yi gagarumin biki na bude ofishin bayan  da a halin yanzu aka bude shi ba a hukumance ba.

Dama dai kungiyar ta Hamas tana da wakilci a cikin wasu kasashen wannan yankin da  su ka hada Iran da Lebanon da kuma Turkiya.

Babban Ofishin siyasa na kungiyar Hamas yana a birnin Doha ne na kasar Qatar, inda shugabanta  Sheikh Isma’ila Haniyyah yake tafiyar da shi.

Tun bayan da HKI ta shekanta yaki akan Gaza, batun Falasdinu da kare hakkokinsu ya sake dawowa da karfi a cikin kasashen wannan yankin na yammacin duniya da kuma duniya baki daya.

Kasashe da daman a duniya sun yi furuci da gwamnatin Falasdinu, ta karsehnsu ita ce Armenia.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments