Search
Close this search box.

Kungiyar Gwagwarmaya Ta Hizbullah Ta Yi Ruwan Bama-Bamai Kan Sansanonin H.K.Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Lebanon ta kaddamar da hare-haren bama-bamai a kan sansanonin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Lebanon ta kaddamar da hare-haren bama-bamai a kan sansanonin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila

Kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi ta kasar Labanon tana ci gaba da kai hare-hare kan sassa daban-daban na haramtacciyar kasar Isra’ila domin nuna goyon baya ga al’ummar Falastinu da ake zalunta kuma suke ci gaba da yin tsayin daka a yankin Zirin Gaza, tare da nuna goyon bayan ga jajircewar Falasdinawa, da kuma mayar da martani da suke yi ga hare-haren da sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suke ci gaba da kai wa kan kauyuka da garuruwan kasar Lebanon.

Haka nan mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullahi sun kai hari kan wata cibiyar tsarin fasaha ta yahudawan sahayoniyya a yankin Metulla, ta hanyar wani jirgin sama mai saukar ungulu, inda suka tarwatsa cibiyar lamarin da ya kai ga tashin mummunar gobara a cibiyar.

Kamar yadda mayakan kungiyar gwagwarmayar Musuluncin suka yi amfani da rokokin Katyusha, wajen kaddamar da hare-hare kan sansanonin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila da suke yankin “Margaliot”.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments