Babban jami’an kungiyar Tarayyar Turai kan Harkokin Waje ya yaba da shawarar da Kotun Duniya (ICJ) ta bayar game da Isra’ila.
Josep Borrell ya ce gabatar da wadannan shawarwarin ya yi daidai da matsayin kungiyar Tarayyar Turai da kuma kudurorin Majalisar Dinkin Duniya dangane da matsayin yankunan Falasdinawa da Isra’ila mamaye.
“A cikin duniyar yau da keta dokokin kasa da kasa ke karuwa, kuma yake bazuwa kamar wutar daji, aikinmu ne day a rataya kanmu mu tabbatar da cewa an yi aiki da dukkanin hukuncin ICJ,” in ji Borrell a kan dandalin X.
A ranar Juma’a kotun kasa da kasa ta ce “ci gaba da kasancewar Isra’ila a yankin Falasdinawa da ta mamaye haramun ne.
Kotun , ICJ ta ce, “yana cikin wani nauyi” da ya rataya kan Isra’ila ta kawo karshen mamayar yankunan Falastinawa cikin sauri-sauri.”
A shekarar 1967 ne sojojin Isra’ila suka mamaye yammacin kogin Jordan da zirin Gaza da kuma gabashin al-Quds, wuraren da Falasdinawa ke son kafa kasa mai cin gashin kai a nan gaba.
Wannan hukunci mai shafuka 83 da shugaban ICJ Nawaf Salam ya karanta ya bayyana jerin manufofin da kotun ta ce sun saba wa dokokin kasa da kasa da suka hada da gine-gine da fadada matsugunan Isra’ila a gabar yammacin kogin Jordan da kuma gabashin birnin Quds.