Kungiyar ECOWAS Ta Sanya Wa’adi Ga Kasashen Da Aka Yi Juyin Mulki A Cikinsu Na Dawowa Cikinta

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta sanyawa kasashe uku da aka yi juyin mulki a cikinsu da su dawo cikin kungiyar zuwa

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS ta sanyawa kasashe uku da aka yi juyin mulki a cikinsu da su dawo cikin kungiyar zuwa ranar 29 ga watan Yulin shekara ta 2025 mai kamawa. Ko kuma kungiyar ta sallamesu daga cikinta.

Shafin yanar gizo na labarai ‘AFRICA NEW” ya nakalto shugaban kungiyar Omar Touray yana fadar haka a taron kungiyar a yau litinin. Ya kuma kara da cewa kofa a bude take ga wadannan kasashe uku na dawowa cikin kungiyar zuwa wa’adin da ta ayyana. ko kuma kungiyar ta sallamesu kwata-kwata daga cikinta.

Mutane a kasashen kungiyar ECOWAS dai suna da damar shiga kasashen 15 ba tare da ViSA ba, sannan akwai hanyoyi da dama da suke amfanar juna a cikinta.

Kasashen Mali, Niger da Burkina Faso ne suka fice daga kungiyar tare da zarginta da dora masu takunkuman tattalin arziki, bayan da sojoji suka kwace mulki a kasashen. Har’ila yau kasashen sun zargi kasashen kungiyar ECOWAS da rashin lura da matsalolin tsaron da suke fuskanta a kasashensu.

Kungiyar ECOWAS dai, wacce ta kai shekaru 50 da kafuwa, ta ce bata bukatar rasa wata kasa daga cikin kasashen yankin. Kuma a farkon juyin mulkin da aka yi a wadannan kasashe uku ta yi barazanar kifar da gwamnatin Niger da karfi, amma daga baya ta fasa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments