Ministocin harkokin wajen na kasashen kungiyar BRICS ta tattalin arziki sun bude taron kwanaki biyu a birnin Nizhny da ke lardin Novgorod na kasar Rasha a jiya Litinin.
Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa ministocin sun bude taron ne da yin shiru na minti guda don tunawa da shugaban kasar Iran marigayi Sayyid Ibrahim Ra’isi da ministansa na harkokin wajen Dr Hussain Amir Abdullahiyan wadanda suka rasa rayukansu a wan hatsarin jirgin sama a ranar 19 ga watan mayun day a gabata a lardin Azarbaijan ta gabas , arewa maso yammacin kasar Iran.
Labarin ya kara da cewa mukaddashin ministan harkokin wajen kasar Iran Ali Bakiri Kani ne ya wakilci kasar Iran a wannan taron da kasashe 10 wadanda suka hada da Rasha, Brazil, India, China, Afirka ta kudu, Masar, Kenya, Hadaddiyar daular Larabawa, da kuma kasar Saudiya.
Bayan isarsa kasar Rasha Bakiri Kani ya bayyana cewa kasar Iran ta shiga kungiyar BRICS ne tare da kokarin da marigayi shahid Ibrahim Ra’isi da ministansa na harkokin waje Dr shahid Hussain Amir Abdullahiyan suka yi a bangaren.