Shugaban tawagar shiga Tsakani na kasar Yemen Abdul Salam ya bayyana cewa: Yemen ta samu sakon bukatu daga Amurka ta hanyar masarautar Oman, kuma wanda ya sauya matsayinsa Amurka ce, ba Yemen ba.
Ya kara da cewa ikirari da Amurka ta yi na mika wuya, yana nuni ne ga gazawa, saboda Amurka ba zata iya kare jiragen ruwan haramtaciyar kasar Isra’ila daga hare-haren Yemen ba.
Abdul-Salam ya kara da cewa: Fahimtar farko da aka samu tsakanin Amurka da Yemen ba ta da wata alaka da matsayar Yemen kan goyon bayan Gaza, yana mai nuni da cewa za a samu ci gaba ta hanyar da ta dace, tare da jaddada cewa Yemen zata mayar da martani ga duk wani ta’addanci daga ko wane bangare.