Kungiyar Ansarullahi Ta Yemen Ta Jaddada Goyon Baynata Ga Kungiyar Hizbullahi Ta Kasar Lebanon

Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin

Jagoran kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen ya jaddada cewa: Suna tsaye kafada da kafada da kungiyar Hizbullah ta Lebanon kan duk wani yunkuri na kokarin tada zaune tsaye daga ‘yan sahayoniyya

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen, Sayyed Abdulmalik Badr al-Din al-Houthi, ya yi gargadin yadda yunwa ke barazana ga Falasdinawa sama da miliyan biyu a zirin Gaza, wadanda ke fuskantar yunwa a idon dukkanin bil’adama. Yana mai jaddada cewa: Wannan abin kunya ne ga kasashen duniya da kungiyoyin agaji na kasa da kasa.

A jawabin da ya gabatar na zagayowar ranar shelar Falasdinawa kan neman taimakon Falasdinawa dangane da hare-haren wuce gona da irin yahudawan sahayoniyya, Sayyid Al-Houthi ya yi bayani kan sabbin abubuwa da suka shafi wuce gona da iri kan Gaza da kuma al’amuran yanki da na kasa da kasa, inda ya bayyana irin girman bala’in jin kai da al’ummar Falasdinu ke fuskanta a karkashin gwamnatin Amurka da ke mara baya ga gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments