Kungiyar Amnesty Tana Zargin : Gwamantin DRC Da Kungiyar M23 Da Yiyuwar Aikata Lafukan Yaki

Kungiyar kare hakkin bil’aama ta “Amnesty International” ta bayyana cewa; mai yiyuwa ne kungiyar ‘yan tawaye ta m23 da kuma sojojin gwamnatin DRC sun aikata

Kungiyar kare hakkin bil’aama ta “Amnesty International” ta bayyana cewa; mai yiyuwa ne kungiyar ‘yan tawaye ta m23 da kuma sojojin gwamnatin DRC sun aikata laifukan yaki.

A wani rahoto da aka buga a jiya Talata, kungiyar kare hakkin bil’adam ta ce; Kungiyar M23 wacce take samun goyon bayan kasar Rwanda ta kashe mutane da dama, da kuma azabtar da su bayan da ta tsare su.

Kungiyar ta M23 ta kwace iko da yankin gabashin kasar mai cike da albarkatun karkashin kasa da su ka hada Bukavu da Goma.

Tare da cewa an kulla yarjejeniya a tsakanin M23 da gwamnatin DRC sai dai kuma har yanzu suna ci gaba da fada.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments