Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta zargi dakarun kai daukin gaggawa na Sudan da aikata muggan laifukan yaki
Yaki a kasar Sudan tsakanin sojojin kasar da dakarun kai daukin gaggawa ya haifar da hasarar rayuka a tsakanin fararen hula sakamakon kai hare-haren ganganci, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin dan Adam suke ci gaba da la’antar laifuka da keta haddi da hare-haren wuce gona da iri da Dakarun kai daukin gaggawa na Rapid Support Forces suke ci gaba da kai wa kan fararen hula a jihar Al-Jazira da ke tsakiyar Sudan, wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwa da jikkatan daruruwan mutane.
Rahotonni sun bayyana cewa: Fararen hula da dama suna fuskantar luguden wuta a rikicin kasar ta Sudan, yayin da dakarun kai daukin gaggawa suke kaddamar da hare-hare ba kakkautawa kan unguwannin da suke cike da jama’a, inda suke kashe mutane a cikin gidajensu, yayin da wasu suka mutu da jikkata yayin da suke gujewa tashin hankalin domin neman wuraren da suke da aminci.