Kotun kasa da kasa ta ICC ta yi tir da gwamnatin kasar Amurka wacce ta kakabawa al-kalan kotun guda hudu saboda hannu da suke da shi wajen fidda sammacin kama fray ministan HKI Benyamin Natanyahu.
Kotun ta kara da cewa tana goyon bayan alkalanta kuma zata ci gaba da aikinta na tabbatar da adalci a duniya duk tare da abinda suke faskanta. Kotun ta bayyana cewa tana aikinta ne bisa goyon bayan kasashen duniya 125 wadanda suka fito daga dukkan kusruwowin duniya.
Takunkuman dai ya shafi wadannan alkalai su 4 kuma mata. Kuma sun hana ko wanne daga cikinsu, shiga kasar Amurka kuma idan suna da kadarori ko kudade gwamnatin Amurka ta kwace su.
A cikin watan Nuwamban shekara ta 2024 ne dai kotun ta ICC wacce take zama a birnin Haque ta fidda sammacin kama Firay ministan HKI Benyamin Natanyahu da kuma tsohon ministan yakin kasar Yoav Galant saboda zargin aikata laifukan yaki a Gaza.