Wata kotu a Saudiyya ta yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari ga wani jami’in kasar da aka samu da laifin cin hanci da rashawa
Hukumomin Saudiyya sun sanar da samun Laftanar Janar Khaled bin Qarar Al-Harbi, tsohon Daraktan Tsaron Jama’a da laifin cin hanci da rashawa da ake tuhumarsa da shi.
Ma’aikatar harkokin cikin gida ta Saudiyya ta watsa rahoton cewa: An yanke hukuncin daurin shekaru 10 a gidan yari kan Laftanar Janar Khaled bin Qarar Al-Harbi, da kuma tarar biyan kudi Riyal miliyan daya, kan laifin yin amfani da tasirin aikinsa don masalahar kansa, da kuma laifin yin amfani da kwangilolin gwamnati wajen wawure dukiyar jama’a.
Rahotonni sun bayyana cewa: Hukumar sa ido da yaki da cin hanci da rashawa ta Saudiyya ta fara gudanar da bincike kan Laftanar Janar Khalid bin Qarar Al-Harbi, tare da mika shi ga kotun ta musamman da take tantance girman laifuffuka, kuma ta yanke masa hukuncin karshe kan matsayin laifinsa.