Kotu A Kasar Finland Ta Yanke Hukunci Kan Simon Ekpa Na Shekaru 6 A Gidan Yari

Rahotanni sun bayyana cewa Kotu a kasar Finland ta yanke wa dan Najeriya mai ‘rajin kafa kasar Biyafara’, Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a

Rahotanni sun bayyana cewa Kotu a kasar Finland ta yanke wa dan Najeriya mai ‘rajin kafa kasar Biyafara’, Simon Ekpa hukuncin daurin shekaru shida a gidan yari bisa laifukan ta’addanci.

Kotun ta same shi da laifin koƙarin harzuka jama’a da niyyar ta’addanci da kuma shiga cikin ayyukan kungiyar ta’addanci.

Haka kuma ta same shi da laifukan zamba ta haraji da kuma karya doka wanda hakan ya sanya kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekara shida a gidan yari.

Kotun ta bayyana cewa Ekpa ya yi kokarin karfafa rajin kafa yankin Biyafara a kudancin Najeriya ta haramtacciyar hanya tsakanin watan Agustan 2021 zuwa Nuwamban 2024.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted