Kotu A Faransa Ta Yanke Hukumci Zama Gidan Yari Ga Tsohon Shugaban Kasar Nicola Sarkozi

A yau  ne Tsohon shugaban kasar faransa Nicola sarkozi zai fara zama a gidan yari na tsawon shekara biyar, bayan da da aka same shi

A yau  ne Tsohon shugaban kasar faransa Nicola sarkozi zai fara zama a gidan yari na tsawon shekara biyar, bayan da da aka same shi da laifin hada baki a watan da ya gabata kan badakkalar kudaden yakin neman zabe daga kasar libiya a zaben shugaban kasa na shekara ta 2007 wanda ya sanya ya zama tsohon shugaban kasa na farko daga wata kasa ta tarayyar turai da zai taba zama a ginda yari,

Wanan hukumcin dai ya faro ne daga zargin da aka yi wa gwamnatin muammar ghaddafi ta libiya na bada wasu kudade ba bisa ka’ida ba a yakin neman zaben Sarkozy a shekara ta 2007 ,

 Alkalan faransa sun yanke wannan hukumcin cewa tsohon shugaban kasar ya shiga wata makarkashiya don boye wadannan kudade, duk da yake cewa an wanke shi da laifin yin amfani da kudaden libiya kai tsaye , da kuma zargin cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kudaden alumma.

Wanan lamarin bai kawar da tasirin sarkozi a cikin jamiyyar masu ra’ayin mazan jiya ba ta faransa, a yan kwanakin nan ne dansa yayi kira ga magoya bayansa da su yi zang-zangar hadin guiwa don  nuna goyon bayansu gare shi, da kuma nuna irin rawar da yake takawa a fagen yancin faransawa duk da matsalolin shar’ia da yake fuskanta.

Magoya bayansa da dama na ganin cewa wannan lamarin yana da alaka da siyasa , yayin da wasu kuma ke ganin ya fallasa irin abubuwan dake tsakanin yan siyasar yammacin duniya da gwamnatin gaddafi,  kafin tsoma bakin kungiyar tsaro ta nato a libiya a shekara ta 2011.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted