Jakadun kasashen larabawa da kuma na wasu kasashen duniya sun bayyana rashin amincewarsu da shirin shugaban kasar Amurka Donal Trump na korar Falasdinawa daga yankin Zirin gaza, saun kuma bayyana hakan a matsayin wanda ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Shirin Trump na korar Falasdinawa daga Gaza dai ya fusata kasashen duniya musamman kasashen larabawa da musulmi, sun kuma ki amincewa da duk wani abu da zai sauyawa Falasdinawa kasarsu.
Wannan yana faruwa ne bayan da HKI ta kasa kwace zirin Gazar a hannun mayakan Hamas da kawayenta na wasu kungiyoyi masu gwagwarmaya a yankin.
Amurka tana son abinda yahudawan basu same shi a yaki ba Trump ya zo ya kwace shi ya mika masu ba tare da wata wahala ba. Sun ki amincewa da hakanne don ya sabawa doka ta 49 na MDD ta shekara 1949, inji Al-Bannai wanda yake magana a madadin kasashen laraba.
Kungiyar kasashen larabawa dai ta ki amincewa da hakan sannan ta kuma sami cikekken goyon bayan kungiyar OIC ta kasashen musulmi da kuma kungiyar yan ba ruwammu, wato ‘the Non-Aligned Movement’ wato (NAM) a takaice..