Kasashen Kungiyar Shanhai Sun Rattaba Hannu Kan Yarjeniyar Aiki Tare A Bangaren Makamashi

Kasashen kungiyar ‘Shanghai Cooperation Organization’ ko (SCO) sun rattaba hannu kan yarjeniyar aiki tare don samarwa da kuma rarraba makamashi a tsakanin kasashen kungiyar. Kamfanindillancin

Kasashen  kungiyar ‘Shanghai Cooperation Organization’ ko (SCO) sun rattaba hannu kan yarjeniyar aiki tare don samarwa da kuma rarraba makamashi a tsakanin kasashen kungiyar.

Kamfanindillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Ali Akbar Mehraniyan ministan makamashi na kasar Iran yana fadar haka a jiya jumma’a  bayan an kamala taron ministocin makamashi na kungiyar karo na 4 a kasar China.

Mehrniyan ya kara da cewa yarjeniyar ta bukaci kasashen kungiyar su samarda makamashi su rarrabashi sannan su sarrafashi a tsakanin kasashen kungiyar.

Banda haka hanyoyin samar da makamashin sun hada da hydrocabone, lantarki, makamashin da ake iya sake sarrafasu, da kuma makamashin nukliya.

Labarin ya kara da cewa JMI tana iya zama kasa wacce zata zama ‘transit’ ko hanyar wucewa don dauko makamashi daga wata kasa ta kungiyar zuwa wata.

Kungiyar  shanhai dai an kafa ta ne a shekara ta 1996 a wani taro na shuwgabannin kasashen China, Rasha, Qazakistan, Qirqizistan da kuma tajakistan. Daga baya kasar Pakistan da shiga cikin kungiyar. Cibiyar Kungiyar mai kasashe 9 a halin yanzu dai yana kasar China.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments