Ministan shari’a na kasar Syria Ahmad al-Sayyid ya yi bayani akan taron kwamitin shari’a na kasashen uku na kasarsa, Iraki da Iraki da su ka yi a raanr Larabar da ta gabata akan hanyoyin bunkasa aiki a fagen fada da ta’addanci.
Ministan shari’ar na kasar Syria ya kara da cewa, matukar duniya tana son zaman lafiya da gaske, to ya zama wajibi ayi aiki da dokokin kasa da kasa ta hanya mafi dacewa. Har ila yau ministan shair’ar na Syria ya yi ishara da abubuwan da suke faruwa a wannan yankin na yammacin Asiya da su ka hada da satar albarkatun kasar Syria, harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancin Iran a Syria,da kuma kisan da aka yi wa mutane a filin saukar jiragen sama na Iraki, tare da bayyana su a matsayin take dokokin kasa da kasa.
Shi kuwa mataimakin ministan shari’a na Iran, Kazim Garib Abadi, ya yi ishara ne da muhimmancin taron na kasashen uku wadanda suke fuskantar hare-haren ta’addanci, kuma kasashen da suke riya cewa suna kare hakkin dan’adam ne suke goyon baya.
Haka nan kuma Garib Abadi ya bayyana harin da aka kai wa karamin ofishin jakadancin na jamhuriyar musulunci ta Iran a Syria da cewa,ta’addanci ne kuma yana cin karo da dokokin kasa da kasa.