Hukumar kare hakkin dan’adam ta MDD ta fitar da bayani a jiya Talata akan yadda jami’an tsaron Amurkan suke amfani da karfi wajen tarwatsa dalibai masu zaman dirshen a harabobin jami’oin kasar.
Shugaban hukumar kare hakkin bil’adam din ta MDD Volker Türk ya bayyana cewa; Da akwai damuwa a cikin yadda aka kama daliban na jami’o’in Amurkan.
Kafafen watsa labarun na Amurkan sun bayyana cewa; ;yan sandan kasar sun rika kwantar da daliban a kasa suna kuma watsa wa wasu barkonon tsohuwa.